Isa ga babban shafi

Hatsarin mota ya kashe mutum 10 a Kanon Najeriya

Mutum 10 ne aka tabbatar sun rasa rayukansu sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da su a jihar Kano da ke Arewacin Najeriya.

Wani hatsarin mota
Wani hatsarin mota Tristan Savatier/Getty Images
Talla

Hukumomi a jihar sun ce, hatsarin ya faru ne ranar Asabar din da ta wuce, lokacin da motar dauke da fasinjoji ta fada  madatsar ruwa ta Fade da ke yankin karamar hukumar Gwarzo.

Jami'in hulda da jama'a na hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Yusuf Abdullahi ya shaidawa RFI cewa motar kirar Golf ta kwace a hannun direbanta ne sakamakon fashewar taya abin da ya kai ga fadawarta madatsar ruwan ta Fade.

Babban jami'in ya kuma tabbatar da cewa an samu nasarar ceto mutum uku daga cikin fasinjojin da suka fada ruwan, inda mutum 10 daga cikinsu suka rasu.

Rahotanni sun tabbatar da cewa mutanen na kan hanyarsu ta zuwa jihar Katsina daga Kano ne, lokacin da al'amarin ya rutsa da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.