Isa ga babban shafi

Za mu ci gaba da taimaka wa Turkiya ta fannin tsaro - Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya bai wa Turkiya tabbacin cewa, Najeriya za ta ci gaba da taimaka ma ta a yakin da take yi da ayyukan ta’addanci, yayin da ya yi tur da harin ta’addancin da aka kai birnin Santanbul a Lahadin nan.

Shugaba Buhari tare da takwaransa na Turkiya, Erdogan
Shugaba Buhari tare da takwaransa na Turkiya, Erdogan naij.com
Talla

Buhari ya yi tur da harin wanda ya lakume rayukan mutane 6 tare da jikkata wasu gommai a kan titin Istiklal mai cike da zirga-zirgar jama’a a tsakiyar birnin Santanbul.

Wata sanarwa da mai magana da yawun Buhari Malam Garba Shehu ya fitar, ta bayyana harin a matsayin abin kyama da kuma rashin jarumta.

Najeriya dai na cikin jerin kasashen Afrika da ke fama da matsalolin tsaro da suka hada da hare-haren Boko Haram da kuma ‘yan bindigar da ke satar mutane suna karbar kudin fansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.