Isa ga babban shafi

Najeriya: 'Yan bindiga sun sace wani hakimi da mutane 6 a Zamfara

‘Yan bindiga sun awon gaba da hakimin gundumar Kwangami a karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya tare da wasu mutane 6.

'Yan bindiga na ci gaba da addabar mutane a yankin arewacin Najeriya.
'Yan bindiga na ci gaba da addabar mutane a yankin arewacin Najeriya. The Guardian Nigeria
Talla

Majiyoyi daga yankin sun ce ‘yan bindigar sun shigo ne da manyan makamai a jiya Litinin, inda suka jefa al’ummar kauyen cikin rudani, kuma suka dauke basaraken, Alhaji Muhammad Galadima.

Sun kara da cewa ‘yan ta’addan sun bi wadannan mutane har gidajensu ne suka dauke su.

A waje daya kuma, ‘yan bindiga ssun sako mutane 6  da suka sace a kauyen Kazauda na karamar hukumar Gusau a jihar Zamfara bayan da aka biya Naira miliyan 4 a matsayin kudin fansa.

Kokarin samun kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Muhammed Shehu don karin bayani ya ci tura.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.