Isa ga babban shafi

Sojin Najeriya sun kashe 'yan bindiga da ke girbi a gonakin manoma a Zamfara

Dakarun  rundunar ta musammaan ta Operation Hadarin Daji sun kashe wasu ‘yaan ta’adda a kauyen  Yar Tashar da ke karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara a arewa maso yammacin Najeriya.

Dakarun sojin Najeriya.
Dakarun sojin Najeriya. YouTube
Talla

Rahotanni sun ce ‘yan ta’addan sun gamu da ajalinsu ne a yayin da ske kokarin girbin amfani gona daga wasu gonaki a kauyen.

Daga cikin wadanda dakarun suka kashe har da wani kasurgumin dan bindiga da aka fi sani da Bada, wanda aka ce ya kai hari kasuwar kauyen, inda ya kashe wasu manoma, kafin daga bisani ya garzaya gonakinsu don girbe hatsi.

Wani babban hafsan sojin da ke aiki a yankin, ya ce dakarunsa sun mayar da martani a kan farmakin da wasu ‘yan bindiga suka kai kaauyen Gamraki na gundumar Kwatarkwashi a karamar hukumar  Bungudu ta jihar, indaa suka raba rana da ‘yan ta’addan, har suka kwato wasu mutane 2 da suka sace.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.