Isa ga babban shafi

Ambaliyar ruwa ta kashe mutane fiye da 600 a Najeriya

Sabbin alkaluman da gwamnatin Najeriya ta fitar, sun nuna cewar, sama da mutane 600 suka rasa rayukansu a ambaliyar ruwan daminar bana a Najeriya, wadda ke zama mafi muni cikin shekaru goma.

Yadda ambaliya ta mamaye wasu sassan jihar Kogi a Najeriya, bayan shafe kwanaki ruwan sama na sauka kamar da bakin kwarya.
Yadda ambaliya ta mamaye wasu sassan jihar Kogi a Najeriya, bayan shafe kwanaki ruwan sama na sauka kamar da bakin kwarya. AP - Fatai Campbell
Talla

Ma’aikatar ayyukan jin kai ta Najeriya ce ta wallafa sabuwar kididdigar a shafinta na Twitter, inda ta ce ambaliyar ruwan ta tilastawa sama da mutane miliyan 1.3 barin gidajensu.

Ministar kula da ayyukan jin kai ta Najeriya Sadiya Umar Faruq, ta ce mutane 603 suka mutu yayin akuwar iftila’in. in ji ministar agajin jin kai Sadiya Umar Farouq.

Ya zuwa yanzu dai, ambaliyar ta lalata gidaje sama da 82,000 da kuma gonakin da fadinsu ya kai kusan kadada 272,000.

A shekarar 2012, mutane 363 ne suka mutu yayin da wasu sama da miliyan 2.1 suka rasa muhallansu sakamakon ambaliyar ruwan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.