Isa ga babban shafi

NEMA ta yi hasashen fuskantar karin ambaliyar ruwa a jihohin Najeriya 14

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya, NEMA ta yi gargadin yiwuwar fuskantar ambaliyar ruwa a wasu jihohin kasar 14 sakamakon tumbatsar kogunan Niger da Benue.

Wani yakin jihar Adamawa da ambaliyar ruwa ta mamaye.
Wani yakin jihar Adamawa da ambaliyar ruwa ta mamaye. News Agency of Nigeria (NAN)
Talla

Gargadin wanda NEMA ta fitar da hadin gwiwar hukumar da ke kula da koguna ta kasar sun ce ambaliyar za ta shafi jihohin Adamawa da Taraba da Benue da Neja da Nassarawa da Kebbi da kuma Kogi baya ga yankin Neja Delta da Edo da Delta da Anambra da Cross River da kuma Bayelsa.

A jawabinsa gaban manema labarai, darakta janar na hukumar NEMA, Mustapha Habib Ahmed ya bukaci gwamnatocin jihohin da ambaliyar za ta shafa su dauki matakan sauya matsugunan al’ummomin da ke cikin hadari don basu kariya daga ambaliyar.

Mustapha Habib Ahmed ya ce a zantawar da ya yi da hukumar kula da koguna ta Najeriya, sun tabbatar mishi cewa masu kula da madatsar ruwa ta Lagdo a Kamaru sun saki wani adadi na ruwa daga ma’adanarsu ranar 13 ga watan da muke ciki na Satumba, wanda kai tsaye ruwan zai shiga kogin Benue.

A cewar NEMA shigar ruwan cikin kogin na Benue zai haddasa tumbatsar da za ta kai ga ambaliya wadda za ta shafi jihohin 14.

Hukumar kula da koguna ta Najeriya NIHSA ta bada tabbacin cewa shigowar ruwan daga Kamaru yanzu haka ya cika ma’adanan ruwan da kasar ke da su da suka kunshi Kainji Jebba da kuma Shiroro wadanda ake sa ran suma su tumbatsa daga yanzu zuwa karshen watan Oktoba mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.