Isa ga babban shafi

NIMET ta yi hasashen kakkarfan ruwan sama a jihohin arewacin Najeriya 5 da Abuja

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya NIMET ta yi hasashen fuskantar kakkarfan ruwan sama na tsawon kwanaki 4 babu kakkautawa a wasu jihohin arewacin kasar 5 da kuma birnin Abuja fadar gwamnatin kasar. 

 Tun kafin gargadin na NIMET dai tuni wasu jihohin Najeriyar musamman a arewaci ke fuskantar ambaliyar bayan kakkarfan ruwan saman kwanaki ba kakkautawa.
Tun kafin gargadin na NIMET dai tuni wasu jihohin Najeriyar musamman a arewaci ke fuskantar ambaliyar bayan kakkarfan ruwan saman kwanaki ba kakkautawa. BOUREIMA HAMA / AFP
Talla

Cikin rahoton hasashen yanayin da hukumar ta NIMET ta fitar ta ce jihohin da za su fuskanci wannan ruwa na tsawon kwanaki 4 ba tare da kakkautawa ba sun kunshi Kaduna da Neja da Bauchi da Pulato da kuma jihar Nassarawa baya ga birnin Tarayyar kasar.

Rahoton na NIMET ya kuma yi hasashen fuskantar madaidaicin ruwan sama a wasu jihohin Najeriya daga kudanci da arewaci da suka kunshi, Kwara da Oyo da Kogi da Ekiti da Ondo baya da Sokoto da Katsina da Zamfara.

Sauran jihohin da za su fuskanci mamakon ruwan sun hada da Kebbi da Kano da Jigawa da Yobe Borno da Gombe da Adamawa da Taraba da Benue da Cross River da Akwa Ibom kana Ebonyi da Enugu da Abia da Imo da Anambra da Rivers da Edo da kuma jihar Delta.

Hukumar ta NIMET ta bukaci daukar matakan gaggawa don kaucewa fuskantar ambaliya musamman la'akari da cewa dukkanin jihohin da ta lissafa kama daga wadanda za su fuskanci mamakon ruwan da wadanda za su fuskanci madaidaici da kuma kakkarfa, kowannensu zai zo da kakkarfar iska.

Wannan rahoto na zuwa ne a dai dai lokacin da ambaliyar ruwa a jiya litinin ta kashe mutane 3 tare da raba iyalai 495 da muhallansu.

Masana dai na ci gaba da gargadin jama'a kan muhimmancin yashe magudanan ruwa da kuma kaucewa tuki a cikin ruwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.