Isa ga babban shafi

NIMET ta yi hasashen fuskantar ambaliya a wasu jihohin Najeriya

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya NIMET ta ce akwai yiwuwar fuskantar ambaliyar ruwa a sassan jihohin Borno da Kebbi da Sokoto da kuma Bayelsa baya ga jihar Delta a cikin kwanaki masu zuwa, dai dai lokacin da damuna ke kara karfi a sassan kasar.

Wani yanki da ke fama da matsalar ambaliyar ruwa.
Wani yanki da ke fama da matsalar ambaliyar ruwa. BOUREIMA HAMA / AFP
Talla

Hukumar ta ce binciken da ta gudanar ta wajen yin nazari a kan danshin kasar ya nuna cewa wasu sassan jihohin da ta ambata suna cikin hatsarin fuskantar ambaliya, saboda kakkarfan ruwan sama ba kakkautawa da yankunan ke fuskanta.

Zuwa yanzu dai ambaliyar ruwa ta tsananta a yankunan arewacin Najeriya bayan shafe tsawon kwanaki ana tafka ruwa ba kakkautawa.

Cikin sanarwar da NIMET ta fitar ta bukaci daukar matakan kariya da nufin kaucewa fuskantar ambaliyar tare da zama cikin shirin ko ta kwana.

A cewar hukumar akwai hasashen samun kakkarfan ruwan sama nan da 'yan kwanaki kalilan a yankunan jihohin da ta lissafi da suka kunshi kaso mai yawa a arewacin kasar da kuma wasu tsiraru daga kudanci.

Yanzu haka ambaliyar ruwan ta yi mummunan ta'adi a wasu kauyukan jihohin Jigawa da Sokoto, biyo bayan ruwan sama da ake kwararawa a cikin kwanakin nan inda a Jigawa kadai ta kashe mutane fiye da 50 baya ga rushe tarin gidaje.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.