Isa ga babban shafi

Ambaliyar ruwa ta kashe mutane 15 a Nijar

Alkalumma da hukumar kwana-kwana da kuma kare lafiyar al’umma ta fitar a jamhuriyar Nijar, na nuni da cewa adadin wadanda suka rasa rayukansu sanadiyyar ambaliyar ruwa sun kai mutane 15 a daminar bana kawai.

Yankuna da dama sun yi fama da ambaliyar ruwa a Nijar
Yankuna da dama sun yi fama da ambaliyar ruwa a Nijar © guardian.ng
Talla

Alkalumman da hukumar ta fitar na nuni da cewa ko bayan wadannan mutane 15 da suka rasa rayukansu, akwai wasu akalla 22 da suka samu raunuka bayan da gidaje suka rufta a kansu.

Rahotan ya ce a jihar Maradi kawai, an samu asarar rayukan mutane 7, a jihar Damagaram an samu mutane 5 yayin da a Tillaberi, Tawa da kuma Diffa aka samu aka samu mutun guda guda kowannensu.

Kawo yanzu dai ambayar ta yi sanadiyyar raba kusan mutane dubu 19 da muhallansu, yayin da ruwa ya yi awon gaba da makarantu, wuraren ibada, rumbunan ajiye abinci da kuma dabbobi masu tarin yawan a sassan kasar.

Mafi yawan mutanen da suka rasa muhallansu dai na rayuwa ne a cikin makarantun boko, yayin da wasu suka nemi mafaka a wajen danginsu.

Kusan dai a kowace shekara a irin wannan lokaci, ana samun ambaliyar ruwa a kasar ta Nijar, lamarin da mahukunta ke dangantawa da matsalar sauyin yanayi da kuma kin mutunta tsarin fasalta birane.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.