Isa ga babban shafi

Ambaliya ta tono kaburbura kusan 1000 a Neja

Ambaliyar ruwa ta tono kaburbura kusan 1000 a wata makabarta da ke karamar hukumar Mariga a jihar Neja.

Yadda ambaliyar ruwa ta mamaye wasu yankunan Najeriya
Yadda ambaliyar ruwa ta mamaye wasu yankunan Najeriya © REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Bayanai sun ce lamarin ya tayar da hankalin al’ummmar yankin.

Yayin zantawarsa da wakilinmu a jihar Neja Isma’il Abdullahi Karatu, babban limamin Masallacin yankin na Mariga Alhaji Alhassan Musa Na’ibi, ya tabbatar da cewa  kimanin kaburbura 1000 ne ambaliyar ruwan ta shafa.

Limamin yayi karin bayanin cewar makabartar da ta shafe akalla shekaru 60 na kusa ne da wani gulbi, wanda shi ne yayi tumbatsar da ya haifar da iftila’in da aka gani, sakamakon saukar ruwan sama kamar da bakin kwarya, tashin hankalin da ya ce shi ne irinsa na farko da aka gani a tsawon shekaru fiye da 60.

Sai dai wasu mazauna yankin sun danganta aukuwar ambaliyar da ta yi muni da ayyukan masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba, wadanda gwamnati ta dakatar su a fadin jihar ta Neja.

Rahotanni daga sassan Neja dai sun tabbatar da cewa mutane da dama sun rasa rayukansu, yayin da aka tafka hasarar dimbin dukiya a yankunan kananan hukumomin Kontagora, Katcha da kuma Mokwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.