Isa ga babban shafi

NIMET da NIHSA sun yi gargadin fuskantar karin ambaliya a sassan Najeriya

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya NIMET da takwararta ta NIHSA da ke hasashen zubar ruwan sama, sun yi gargadi kan yiwuwar fuskantar matsananciyar ambaliyar ruwa a jihohin shiyyar Arewa ta tsakiya da kudu maso yammacin kasar nan da kwanaki kalilan masu zuwa.

Zuwa yanzu dai, jihohin Najeriya 29 daga cikin 36 ne suka fuskanci matsananciyar ambaliya da ta haddasa asarar dimbin rayuka da tarin dukiya.
Zuwa yanzu dai, jihohin Najeriya 29 daga cikin 36 ne suka fuskanci matsananciyar ambaliya da ta haddasa asarar dimbin rayuka da tarin dukiya. REUTERS - Stringer .
Talla

Darakta Janar na hukumar NIMET farfesa Mansur Bako Matazu ya ce hasashensu ya nuna yiwuwar samun mamakon ruwan sama a yankunan 2 wanda zai zama kari kan ballewar wasu Datsun ruwan kasar lamarin da zai haifar da gagarumar ambaliya.

Hasashen hukumomin biyu na zuwa ne a dai dai lokacin da jihohin Benue da Kogi ke tsaka da fuskantar mummunar ambaliyar ruwan da ta haddasa asarar rayukan jama'a da kuma dimbin dukiya, ambaliyar da bayanai ke cewa ita ce mafi muni da kasar ta gani tun bayan makamanciyarta a shekarar 2012.

Farfesa Bako Matazu ya ce tun a watan Fabuwairun da ya gabata suka yi hasashen samun ambaliyar ruwa a sassan kasar, sannan kuma suna tunasar da al’umma halin da ake ciki a sanarwar hasashen yanayin da su ke fitarwa a kowanne wata.

Farfesa Matazu ya ce a shekaru masu zuwa za a samu ruwan sama mai yawan gaske, wanda hakan ke cikin matsalolin sauyin yanayin da aka fuskanta.

A daminar bana dai, jihohin Najeriya 29 daga cikin 36 da kasar ke dasu ne suka fuskanci ambaliyar ruwa, wadda kuma ta yi sanadiyar mutuwar mutane da dama da lalata dukiyar miliyoyin naira musamman a jihohin arewacin kasar da suka kunshi Taraba da Jigawa da Kogi da kuma jihar Kano.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.