'Yan sanda sun cafke sojojin da ake zargi da kashe fitaccen malami a Yoben Najeriya
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce ta kama wasu sojoji biyu bisa laifin kashe wani malamin addinin Islama, Sheikh Goni Gashua.
Wallafawa ranar:
An kashe Sheikh Gashua ne a daren Juma’a a kusa da Jaji Maji a karamar hukumar Karasuwa da ke jihar Yobe a arewa maso gabashin kasar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Yobe, Dungus Abdulkareem, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ga jaridar PREMIUM TIMES, ya ce nan da ‘yan kwanaki kadan za a fitar da cikakken bayan ikan sojojin.
Ya ce, sojojin biyu sun amsa laifinsu amma har yanzu ana ci gaba da bincike, sai dai yaki bayyana sunayen wadanda aka kama din.
Sai dai wata majiya a Yobe, daga ‘yan kungiyar sintiri ta jihar, ta bayyana yadda aka kashe fitaccen malamin addinin musuluncin.
Jami’in kungiyar ya ce daya daga cikin sojojin ya bukaci malamin ya rage masa hanya ne akan hanyar Nguru, lokacin da yake komawa Yobe daga Kano.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu