Isa ga babban shafi

Ina maraba da Tinubu da Shettima duk da kasancewa ta kirista - Lalong

Shugaban kwamitin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasar Najeriya a Jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu da Kashim Shettima, Gwamnan Jihar Filato Simon Lalong yace yana farin cikin jagorancin kwamitin a matsayin sa na Kirista kuma dan darikar Katolika.

Gwamnan Jihar Filato Barr Solomin Lalung
Gwamnan Jihar Filato Barr Solomin Lalung plateaustate.gov.ng
Talla

Lalong ya shaidawa manema labarai a fadar shugaban kasa cewar an haife shi kuma ya tashi a matsayin dan darikar Katolika, yayin da yake rike da kyauta mafi girma daga ofishin Fafaroma da ake kira ‘Knight of Saint Gregory the Great’, saboda haka Fafaroma bai shaida masa cewar haramun ne jagorancin yakin neman zaben yan takara Musulmi.

Gwamnan yace bayan nadin da aka masa a matsayin jagoran yakin neman zaben, daga cikin wadanda suka tarbe shi a tashar jiragen saman Yakubu Gowon dake Jos, harda wakilan kungiyar Kiristocin Najeriya reshen jihar Filato.

Lalong ya bayyana shakku dangane da wadanda suke ikrarin zama Kiristoci dake adawa da nadin da aka masa, yayin da yayi watsi da wasu shugabannin addinin dake bukatar sa da yayi watsi da mukamin saboda abinda suka kira kin baiwa Kirista damar samun kujerar wanda zai marawa Tinubu baya.

Gwamnan yace yana mutunta kowanne addini, kuma wadanda suka zabe shi ya zama Gwamna sun fito ne daga bangarorin addinai daban daban.

Lalong yace ya ziyarci fadar shugaban kasa ne domin godewa Muhammadu Buhari akan akan ayyukan raya kasar da ya amince ayi a Jihar Filato tare da afuwar da aka yiwa tsohon Gwamnan Jihar Joshua Dariye da tsohon Gwamnan Taraba Jolly Nyame.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.