Isa ga babban shafi

Zaben 2023: Tinubu ya zabi Kashim Shettima a matsayin mataimakinsa

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya Asiwaju Bola Tinubu, ya bayyana Sanata Kashim Shettima, tsohon gwamnan jihar Borno, a matsayin wanda zai yi masa mataimaki a zaben shekara ta 2023.

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, tare da tsohon gwamnan jihar Borno Kashim Shettima daga tsakiya.
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, tare da tsohon gwamnan jihar Borno Kashim Shettima daga tsakiya. © Daily Trust
Talla

Tinubu ya bayyana hakan ne a yayin tattaunawa da manema labarai a ziyarar da ya kai wa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a garin Daura na jihar Katsina a yau Lahadi.

A baya dai wata majiya da kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ya ruwaito, ta bayyana cewa Tinubu ya zabi Shettima a matsayin mataimakinsa, kuma zai bayyana hakan a cikin makon da za a shiga.

A karshen watan Yunin da ya gabata, Tinubu, ya ce ya mika sunan wanda ya zaba a matsayin mataimakinsa, ga hukumar zabe mai zaman kanta INEC, ba tare da bayyana sunansa ba.

Kafin sanarwar waccan lokacin, dan takarar jam'iyyar APC mai mulki, ya zabi Alhaji Kabir Ibrahim Masari daga jihar Katsina ne a matsayin wanda zai tsaya takarar mataimakinsa domin ya cika wa’adin da hukumar INEC ta kayyade, sai dai an tsayar da Masari takarar ne na wucin gadi ne har zuwa lokacin da za a kammala tuntubar juna tsakanin masu ruwa da tsaki kan wanda za a tabbatarwa takarar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.