Najeriya: Zamfara ta bai wa dan bindiga sarauta don samun zaman lafiya
A Najeriya, masarautar ‘Yan Doton Daji dake jihar Zamfara a arewa maso yammacin kasar ta nada wa wani kasurgumin dan bindigan nan da ake kira Ada Aliero sarautar Sarkin Fulanin Yandoto.
Wallafawa ranar:
An gudanar da bikin nadin ne duk kuwa da cewa an sanar da dakatar da shi tun da farko bisa wani sako da aka samu daga hukumomin jihar, kamar yadda jaridar ‘Daily Trust’ da ake wallafawa a Najeriya ta ruwaito.
Sai dai duk da haka bikin ya samu halartar shugaban karamar hukumar Tsafe da kwamishinan tsaro na jijhar Zamfara, Ibrahim Mamman Tsafe.
Wasu majiyoyi sun ce an yanke shawarar yi wa Aleiro wannan sarautar ce sakamakon rawar da ya taka wajen cimma yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin masauratar da ‘yan bindiga da ke addabar karamar hukumar Tsafe.
Majiyoyi daga fadar kuwa sun ce gwamnatin jihar ta yi umurnin dakatar da nadin ne bisa fargabar yadda al’umma za su dauki lamarin, bayan da wasu kafafen yada labarai suka bankado shirin.
Sai dai shugaban kwamitin kwance damarar 'yan bindiga a jihar Zamfara ya tabbatar wa da sashen Hausa na RFI cewa lallai an yi wannan nadi ne don a samu zaman lafiya mai dorewa a jihar, duba da cewa babu wani zabi da ya wuce haka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu