Isa ga babban shafi

Najeriya: Wani Daliget din APC ya mutu a Abuja gabanin zaben fidda gwani

Shirye shirye sun kammala dan soma gudanar da zaben fidda gwanin jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya a filin taron Eagle Squre dake Abuja fadar gwamnatin kasar.

Shirye -shirye ya kankama a filin Eagles Square, inda ake gudanar da zaben fid da gwani na jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya.
Shirye -shirye ya kankama a filin Eagles Square, inda ake gudanar da zaben fid da gwani na jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya. © apc
Talla

To sai dai haryanzu babu tabbas game da mutumin da zai iya samun tikitin takarar shugabancin kasar na zabe mai zuwa, lura da yadda kowwa ya ja daga cikin mutane 4 da suka rage.

Ana takarar ne tsakanin mataimakin shugaban kasa farfesa Yemi Osinbajo, da Asiwaju Bola Tinubu da kuma Rotimi Amechi sai kuma gwamnan jihar Kogi yahaya Bello da abaya ake guna gunin janyewar sa.

Mutuwar Daliget

Wakilin mu Mohammed Kabir Yusuf dake filin taron ya tabbatar da mutuwar wani daliget na APC a Abuja babban birnin kasar wanda ya je halartar zaben na fid da gwani.

Rahotanni  na cewa daliget din mai suna Isa Baba-Buji, dan asalin Jihar Jigawa ne kuma ya rasu ne a lokacin da yake karya kumallo kafin tafiya dandalin Eagle Square.

Jami'an EFCC sun kutsa Eagles Square

Jami'an hukumar yaki da cin hanci da Rashawa EFCC sun hallara dandalin Eagles Square domin ganin cewa ba'a baiwa daliget kudade ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.