Gwamnan Sokoto ya janye dokar hana fita ta sa'o'i 24
Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya janye dokar hana fita da ya kafa a cikin birnin Sokoto, matakin da ya ce ya fara aiki nan take, inda ya kuma haramta duk wani nau'i na gangami, ko jerin gwano a jihar har sai abinda hali yayi.
Wallafawa ranar:
Gwamnan ya ce matakin ya biyo bayan tuntubar juna da hukumomin tsaro da abin ya shafa.
An dai kafa dokar hana fita ta sa'o'i 24 a birnin Sokoto ne bayan wata zanga-zanga da ta yi sanadin mutuwar mutum daya a jihar, kamar yadda wakilinmu ya tabbatar, yayin da wasu da dama suka jikkata a yayin zanga-zangar da ta janyo kafa dokar hana fitar a birnin Sokoto da kewayensa.
Masu zanga-zangar sun nemi sakin mutane biyu da ake zargi da kashe Deborah Samuel, bisa tuhumarta da batanci ga Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi.nura
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu