Isa ga babban shafi

Dokar hana fita na cigaba da aiki a Sokoto

Dokar hana fita na cigaba da aiki a jihar Sokoto da ke arewacin Najeriya, wadda gwamnan Aminu Waziri Tambuwal ya kafa a karshen  domin tabbatar da zaman lafiya, sakamakon zanga-zangar da matasa suka gudanar, kan neman sakin wasu samari 2 da jami’an tsaro suka kama, sakamakon zarginsu da ake da kisan Deborah Emmanuel, dalibar ta yi batanci ga Annabi Muhd, tsira da amincin su tabbata a gare shi.

Gwamnan JIhar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal.
Gwamnan JIhar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal. © Daily Trust
Talla

Wakilinmu a jihar ta Sokoto ya shaida mana cewar, mutum 1 ya rasa ransa yayin da wasu da dama suka jikkata a yayin zanga-zangar da ta janyo kafa dokar hana fitar da a yanzu haka ke aiki, domin tabbatar da doka da oda.

A baya bayan nan, kungiyar Kiristoci ta Najeriya CAN ta umarci dukkanin mabobinta da su gudanar da tarukan alhini, da addu’a da kuma zanga-zangar lumana, amma a mujami’un da suke da fadi ba kan tituna ba, a bisa kashe Deborah Emmanuel da fusatattun matsa suka yi sakamakon batancin da ta yi wa Annabi Muhd tsira da amincin A su tabbata a gare shi.

Mujami’ar Katolika ta Holy Family a jihar Sokoto da ke Najeriya ta ce babu wanda aka kashe a yayin harin da wasu matasa Musulmi suka kai wa cocin a ranar Asabar.

Wata sanarwa da ta sami sa hannun daraktan watsa labarai na majami’ar, Christopher Omotosho ta ce sai dai masu zanga zangar sun lalata wani sashi na majami’ar, da kuma wani coci a cikin garin na Sokoto.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.