Isa ga babban shafi
Najeriya -Sokoto

Zanga-zanga: An sanya dokar hana fita ta sa'o'i 24 a Sokoto

Mahukunta a jihar Sokoto dake arewa maso yammacin Najeriya, sun ayyana dokar hana fita na tsawon sa’o’i 24, biyo bayan mummunar zanga-zangar da matasa suka gudanar, ta neman sakin wasu samari 2 da hukumomi suka kama, sakamakon zarginsu da ake da kisan Deborah Emmanuel, wadda ta yi batanci ga Annabi Muhammad, tsira da aminncin Allah su tabbata a gare shi.

Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal.
Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal. © Twitter / @AWTambuwal
Talla

A wata sanarwa da ya fitar a yau Asabar, gwamman jihar, Aminu Waziri Tambuwal ya ce dokar hana fitar ta zama wajibi don maido da doka da oda, biyo bayan lamarin da ya taso daga kisan dalibar kwaleji ilimi ta Shehu Shagari a jihar.

Tambuwar ya yi kira ga al’ummar jihar da su kauce wa tashin tashina, ta wajen yin biyayya da doka, inda ya roki ilahirin al’ummar da ke waje su koma gidajensu.

Masu zanga zangar suna rike da kwalaye dauke da rubuce rubucen da ke neman hukuma su saki wadanda suka kama bisa zargin kisan dalibar da ta yi batanci ga addibnin Musulunci.

Rahotanni sun ce halin yanzu jami’an tsaro ne ake gani a dukkanin sassan kwaryar birnin Sokoto, wadanda ke sintirin tabbatar da an kiyaye dokar

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.