Isa ga babban shafi
Najeriya-Sokoto

Katolika a Sokoto ta ce ba wanda ya mutu a harin masu zanga zanga

Majami’ar Katolika ta Holy Family a jihar Sokoto da ke Najeriya ta ce babu wanda aka kashe a yayin harin da wasu matasa Musulmi suka kai wa cocin a jiya Asabar.

Majami'ar Katolika ta Sokoto.
Majami'ar Katolika ta Sokoto. © facebook.com
Talla

Wata sanarwa da ta sami sa hannun daraktan watsa labarai na majami’ar, Christopher Omotosho ta ce sai dai masu zanga zangar sun lalata wani sashi na majami’ar, da kuma wani coci a cikin Sokoto.

Sanarwar ta ce masu gadin majami’ar sun dakile masu zanga zangar kafin su aikata barna dayawa.

Matasa da suka fusata ne suka bazama titunan Sokoto, inda suke zanga zangar neman a saki wadanda aka kama sakamakon zargin su da ake musu na kisan wata  daliba da ta yi batanci ga Annabi Muhammad Tsira da Aminci Allah su tabata a gare shi.

A kokarinta na samar da sauki ga al’ummar jihar, gwamnatin Sokoto ta ayyana dokar hana fita ta tsawon sa’o’i 24 a kwaryar jihar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.