Isa ga babban shafi

NRC ta yi bayani kan harin da aka kaiwa jirginta a tsakanin Abuja da Kaduna

Hukumar kula da sufurin jiragen kasa ta Najeriya NRC ta yi karin bayani kan harin da aka kaiwa daya daga cikin jiragen na ta a lokacin da yake kan hanyar zuwa Kaduna daga birnin Abuja a Litinin ta makon jiya, inda ta bayyana cewar zuwa yanzu ba a gano inda fasinjoji 21 suke ba.

Wasu fasinjojin jirgin kasa dake sufuri tsakanin Abuja da Kaduna a Najeriya.
Wasu fasinjojin jirgin kasa dake sufuri tsakanin Abuja da Kaduna a Najeriya. © Daily Trust
Talla

Yayin da yake gabatar da rahoton da suka tattara, babban daraktan hukumar sufurin jiragen kasan Najeriyar, INjiniya Okhiria Fidet, ya ce jumillar fasinjoji 362 ne a hukumance aka tabbatar suna cikin jirgin da ‘yan ta’adda suka kaiwa farmaki.

Injiniyan ya kara da cewar kawo yanzu sun tabbatar da cewa fasinjoji 170 sun tsira, yayin da 21 suka bace, sai dai bai yi karin bayani akan ragowar fasinjoji 171 ba.

Bayanan farko jim kadan bayan harin da aka kaiwa jirgin kasan a hanyar Abuja zuwa Kaduna a makon jiya dai sun nuna cewar fasinjoji fiye da 900 ne ke cikinsa, yayin da kuma a baya bayan nan, rahoton hukumar sufurin jiragen kasan Najeriya ya nuna cewar jirgin zai iya daukar fasinjoji 840.

Tuni dai aka dakatar da jigilar jiragen kasa a tsakanin birnin na Abuja da Kaduna, har zuwa lokacin da za a kammala gyara titin da ‘yan ta’adda suka dasawa bam, da kuma tabbatar da tsaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.