Isa ga babban shafi
Najeriya

Hari kan jirgin kasa ya haifar da shakku kan shugabancinmu - Gwamnoni

Kungiyar Gwamnonin Najeriya ta yi Allah-wadai da harin ta’addancin da ‘yan bindiga suka kai kan jirgin kasan da ke kan hanyar zuwa Kaduna daga Abuja a ranar Litinin.

Jirgin kasan da 'yan bindiga suka kaiwa hari yayin da yake kan hanyar Abuja. zuwa Kaduna
Jirgin kasan da 'yan bindiga suka kaiwa hari yayin da yake kan hanyar Abuja. zuwa Kaduna © AP
Talla

Cikin wata sanarwa da suka fitar mai dauke da sa hannun shugabansu Kayode Fayemi, Gwamnonin sun koka kan yadda munanan hare-hare ke kara yawa kan ‘yan Najeriya, kuma hakan ke haifar da shakku kan ikonsu na gudanar da mulki, don haka dole ne su farka daga barcin da suke.

Kungiyar Gwamnonin ta nemi wadanda ke da iko da su hanzarta daukar matakan kariya don hana ayyukan barna nan gaba a kan hanyoyin jirgin kasa, hanyoyi, tashoshin jiragen ruwa, da kan iyakokinmu.

Sai dai a bangaren Gwamnan Kaduna malam Nasir El Rufa’i ya bayyana bacin ransa ne kan yadda ya ce rundunar sojin Najeriya ta san inda sansanonin ‘yan bindigar da ke addabar al’ummar jiharsa suke, amma ta ki yi musu ruwan bama-bamai, duk da cewar gwamnati ta ayyana su a matsayin ‘yan ta’adda.

Gwamnan ya kuma bukaci gwamnatin Najeriya da ta kafa sansanonin sojin a yankunan Katari da Rijana wadanda suka yi kaurin suna wajen fuskantar hare-haren ‘yan bindiga a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.