An kashe tare da sace mutane yayin harin jirgin ƙasa a hanyar Abuja zuwa Kaduna
Rahotanni daga Najeriya na cewa an sace fasinjoji da dama bayan harin da wasu 'yan bindiga suka kai kan jirgin kasa da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna a yammacin ranar Litinin, wanda yayi sanadiyar rasa ruyuka da jikkatar wasu.
Wallafawa ranar:
Kunna - 01:39
Fasinjoji da kuma 'yan uwan wasu fasinjojin sun shaida wa RFI cewa lamarin ya yi matukar muni kuma har yazu ba a san takamaiman mutanen da lamarin ya shafa ba.
Wani fasinja da yace a kan idonsa aka harbe wani na kusa da shi, yace sun ga gawar mutane akalla goma, yayin da akayi gurkuwa da mutane da dama.
Kuna iya latsa alamar sauti domin sauraren rahotan waklin mu na Abuja Mohammed Sani Abubakar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu