Isa ga babban shafi
Najeriya - Kaduna

Na taba yin gargadi kan yiwuwar kaiwa jirgin kasa hari - Amaechi

Ministan Sufuri Rotimi Amaechi ya mayar da martani kan harin ta'addancin da aka kaiwa jirgin kasan da ke kan hanyar zuwa Kaduna daga Abuja, inda ya ce ya dadi da yin gargadin cewa za a iya fuskantar irin wannan matsala ta hasarar rayukan da aka gani, idan har ba a dauki kwararan matakan rigakafi ba.

Ministan Sufurin Najeriya Rotimi Amaechi.
Ministan Sufurin Najeriya Rotimi Amaechi. © Twitter/@MinTransportNG
Talla

Ministan ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a lokacin da ya ziyarci inda ta’addancin ya faru.

Amaechi wanda ya ke Magana cikin bacin rai, ya ce   za a iya kaucewa aukuwar tashin hankalin da ya rutsa da aka gani, inda a ce an samar da na’urorin tsaron fasahar zamani, wadanda kudinsu bai zai wuce Naira biliyan 3 ba.

Cikin bayanan da ya yi wa manema labarai, ministan sufurin ya ce yayi gargadin cewa za a iya samun asarar rayuka, abinda kuma ya faru.

Amechi ya kara da cewar mutane takwas sun mutu, wasu 25 suna kwance a asibiti, kuma ba a san adadin wadanda aka sace ba, baya ga hasarar kadarar da aka yin a jirgin kasan kansa da kuma layin dogon.

A ranar Litinin din da ta gabata ‘yan ta’adda suka dasa bam a kan titin jirgin kasan da ke sada birnin Abuja da da kaduna, inda suka kashe mutane akalla takwas da kuma sace wasu fasinjojin masu yawan gaske, koda yake akwai wasu majiyoyin da ke cewar adadin mutanen da suka rasa rayukansu ka iya zarce wanda aka bayyana a hukumance.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.