Isa ga babban shafi
Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta sansanta da kamfanin Twitter

Gwamnatin Najeriya ta sanar da janye matakin haramta ayyukan kamfanin Twitter a kasar, bayan shafe akalla watanni bakwai da dakatar da shi.

Twitter
Twitter AP - Matt Rourke
Talla

Shugaban kwamitin Hukumar Bunkasa Fasahar Sadarwa ta Najeriya, wanda kuma ke jagorantar kwamitin da ke tattaunawa ta kamfanin na Twitter Kashifu Inuwa Abdullahi ne ya sanar da matakin a ranar Laraba.

Cikin sanarwar da ya fitar a Abuja, babban jami’in gwamnatin Najeriya yayi bitar dalilan da suka sanya daukar tsattsauran matakin da gwamnati ta yi akan Twitter, wadanda suka hada da, amfani da dandalin da wasu marasa kishin kasa ke yi wajen yi wa gwamnati zagon kasa, yada labaran karya, da kuma yunkurin rarraba kan ‘yan Najeriya ta hanyar amfani da kabilanci da kuma addini, da dai wasu karin miygun ayyuka.

A ranar 2 ga watan Yunin da ya gabata a shekarar 2021, kamfanin Twitter ya soke sakon da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya wallafa akan ‘ya’yan haramtaciyyar kungiyar IPOB wadanda ke fafutukar kafa kasar Biafra, inda kamfanin ya kuma dakatar da shafin shugaban Najeriyar na wucin gadi.

Kamfanin ya kare kare matakin na sa da cewar, sakon shugaban Najeriyar da ya soke na kunshe da kalaman da suka sabawa ka’ida, sakamakon cewar da yayi, wadanda ke tayar da rikicin Biafra, ba su san tashin hankalin rasa rayuka da hasarar dimbin dukiyar da yakin basasar Najeriya ya haifar ba, inda yayi gargadin cewa su da suka kasance a filin daga tsawon watanni 30 za su ladabtar da su da yaren da za su fahimta.

A ranar 5 ga watan Yunin ne kuma dukkanin masu kafofin sadarwar intanet suka datse kamfanin Twitter a Najeriya, umarnin da gwamnatin kasar ta bayar.

Daga cikin sharuddan da kamfanin na Twitter ya cika a halin yanzu kafin janye haramcin da aka yi masa a Najeriya, akwai yin rajistar gudanar da ayyukansa karkashin dokokin kasar, biyan gwamnati haraji, da kuma dakile wallafar haratattun sakwannin da dokoki suka haramta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.