Isa ga babban shafi
Najeriya-Trump

Trump ya yaba wa Najeriya kan matakin dakatar da Twitter

Tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya yabawa Najeriya dangane da matakin dakatar da kamfanin sadarwa na Twitter da ta yi bayan kamfanin ya goge wani rubutun shugaban kasar Muhammadu Buhari.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayin ganawa da Donald Trump tsohon shugaban Amurk.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayin ganawa da Donald Trump tsohon shugaban Amurk. REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

A wata sanarwa da Donald Trump ya fitar ya ce, ya taya Najeriya murna da suka dauki matakin dakatar da Twitter wadda ya bayyana a matsayin hatsabibin kamfani.

A cewar Donald Trump idan kamfanin na Twitter ba gurbatacce ba ne ta yaya ne a karan kansa zai iya tantance gurbataccen sako da kuma sahihi, har ma ta kai ga gogewa.

Trump wanda ya jima yana fuskantar takun saka da Twitter dangane da makamancin matakin na yiwa rubutunsa kwaskwarima ko kuma gogewa ya bukaci kasashe su dauki matakin dakatar da kamfanin har ma Facebook kana bin da ya kira kin baiwa jama’a damar fadar albarkacin bakinsu.

Tun bayan sakon da Trump ya wallafa a shafinsa na Twitter, da aka yi zargin shi ya tunzura boren Capitol na watan janairu ne Twitter da Facebook baya ga Instagram suka dakatar da tsohon shugaban na Amurka, lamarin da ya rura wutar rikicin da ke tsakaninsa da su.

A cewar Trump Najeriya ta yi dai dai wajen dakatar da kamfanin wanda tsohon shugaban ya ce shi kansa ya so ace a lokacin mulkinsa ya dakatar da kamfanin a Amurka saboda katsalandan din da ya ke yiwa jama'a a al'amuransu.

Yanzu haka dai kamfanin na Twitter ya dakatar da Trump na har abada yayinda Facebook da Instagram suka ce za su janye ta su dakatarwar nan da shekaru 2 masu zuwa.

A Najeriyar dai ana ci gaba da shiga tsakani game da rikicin gwamnati da kamfanin na Twitter tun bayan dakatar da shi a makon jiya, ko da ya ke matakin na ci gaba da fuskantar caccaka daga bangarori daban-daban, ko da ya ke al'ummar kasar da dama na goyon bayan matakin gwamnatin kan lamarin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.