Isa ga babban shafi
Najeriya-Twitter

Najeriya na tattaunawar sulhu da Twitter

Hukumomin Najeriya sun ce sun fara tattaunawa da kamfanin Twitter na Amurka domin warware matsalar da aka samu a tsakanin su bayan dakatar da shi daga aiki a kasar.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. Twitter@BashirAhmaad
Talla

Dakatar da kamfanin ya haifar da muhawar mai zafi tsakanin masu goyan bayan matakin da masu adawa da shi.

Ministan harkokin wajen kasar Geoffrey Onyeama ya tabbatar da tattaunawar bayan ganawa da Jakadun wasu kasashe kan dalilin daukar matakin.

A makon jiya Amurka ta soki lamirin gwamnatin Najeriya a game da dakatar da dandalin sada zumunta na Twitter a kasar, tana mai bayyana matakin a  matsayin sako mara armashi ga al’umar kasar da ma masu zauba jari a cikinta.

A martanin da ta mayar a wata sanarwa, fadar gwamnatin Najeriya ta kare haramcin da ta yi wa Twitter, tana mai cewa dandalin Twitter ya dade yana tabargaza a kasar kuma ba  a daukar mataki

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.