Isa ga babban shafi
NAJERIYA-TSARO

Najeriya ta ce kamfanin Twitter ya amince da sharuddan da ta gindaya masa

Gwamnatin Najeriya tace kamfanin twitter ya amince da daukacin sharidodin da aka gindaya masa kafin bashi sabon umurnin komawa aiki a cikin kasar.

Alamun kamfanin Twitter
Alamun kamfanin Twitter Kirill KUDRYAVTSEV AFP
Talla

Ministan kasa a ma’aikatar kwadago Festus Keyamo wanda ke cikin ‘yan kwamitin da gwamnati ta kafa domin tattaunawa da kamfanin yace sun samu gagarumar ci gaba a ganawar da suke yi.

Keyamo yace matakin da shugaban kasa ya dauka akan kamfanin an dauke shi ne domin inganta danganta tsakanin bangarorin biyu amma ba domin korar sa daga Najeriya ba.

Daga cikin sharidodin da gwamnatin Najeriya ta gindayawa kamfanin twitter akwai bude ofishin sa a cikin kasar wanda zai baiwa ‘yan Najeriya damar kai korafin su da kuma biyan haraji ga gwamnati.

Kamfanin twitter ya harzuka ‘Yan Najeriya lokacin da ya sanar da aniyar sa ta bude ofishin sa a Ghana maimakon Najeriya, kasar dake dauke da miliyoyin jama’ar dake amfani da shi fiye da kowacce kasa a nahiyar Afirka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.