Isa ga babban shafi
Zamfara-'Yan bindiga

Gwamnati ta tabbatar da kisan mutane 200 cikin mako guda a Zamfara

Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da cewa akalla mutane 200 ‘yan bindiga sun kashe tare da raba wasu dubbai da muhallansu, yayin munanan hare-haren da suka kai cikin makon jiya a Jihar Zamfara da ke yankin arewa maso yammacin kasar.

'Yan bindiga sun addabi jihar Zamfara ta Najeriya
'Yan bindiga sun addabi jihar Zamfara ta Najeriya © dailypost
Talla

Ministar kula da ayyukan jin kai a Najeriya Sadiya Umar Farouq ta tabbatar da alkaluman mamatan da ‘yan bindigar suka yi wa kisan gilla ne cikin wata sanarwa ta hannun mai magana da yawunta Nneka Ikem Anibeze a Lahadin da ta gabata, inda ta kara da cewar, fiye da mutane dubu 10 suka rasa muhallansu da ‘yan ta’addan suka kone yayin hare-haren kan wasu kauyukan kananan hukumomin Bukuyyum da Anka a jihar Zamfara.

A ranar Asabar din da ta gabata ne dai i, wasu mazauna yankunan da lamarin ya rutsa da su, suka shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, akalla mutane 140 ‘yan bindigar suka kashe a tsakanin ranakun Laraba zuwa Alhamis.

Ko da yake a na ta bangaren gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana adadin mamatan ne akan mutane 58, bayan da Sarkin Anka ya ce mutane 22 aka kashe a yankinsa, yayin da Sarkin Bukkuyum ya sanar da mutuwar wasu 36, alkaluman da kakakin gwamnatin Zamfara Zailani Bappa ya tabbatar a wata sanarwa da ya fitar da yammacin ranar Asabar.

Ranar Asabar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a ya yi A-wadai da hare-haren ta’addancin a Zamfara, da ya bayyana a matsayin huce fushi kan wadanda basu ji ba basu gani ba, da ‘yan bindigar suka yi, saboda hare-haren da jami’an tsaron suka kaddamar akansu a baya bayan nan.

Wasu majiyoyi sun ce, daruruwan ‘yan ta’addan da suka kaddamar da munanan hare-haren, masu biyayya ne da kasurgumin dan fashin dajin nan Bello Turji, wadanda hare-haren jiragen yakin sojin Najeriya ya tilastawa tserewa daga sansanoninsu da ke dajin Fakai a karamar hukumar Shinkafi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.