Isa ga babban shafi
Najeriya - Abuja

Gwamnatin Najeriya ta musanta cewar Abuja na fuskantar barazanar tsaro

Ministan harkokin cikin gidan Najeriya Rauf Aregbesola ya karyata rahotannin da ke yawo a kafafen yada labarai dangane da cewa bakin ‘yan ta’adda daga kasashen waje na barazanar kai hare-haren ta’addanci a Abuja babban birnin kasar a cikin watan Disamba.

Ministan cikin gidan Najeriya Rauf Aregbesola
Ministan cikin gidan Najeriya Rauf Aregbesola © Twitter / RAUFAAREFBESOLA/OGUNDIRANDOLAPO
Talla

Aregbesola ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai kan sakamakon taron gaggawa na majalisar tsaron Najeriya, wanda shugaban kasar Muhammadu Buhari ya jagoranta a Abuja.

A cewar Ministan, Abuja na cikin kwanciyar hankali da samun cikakken tsaro daga dukkanin wata barazana ta fuskantar hare-haren ta’addanci.

Ministan cikin gidan ya kara da cewar, ba aibu bane a samu bullar wani rahoto da ke jan hankalin hukumomin tsaron Najeriya dangane da wata barazana komai kankantarta, dan haka sanarwar da ta bulla a kwanakin baya kan yiwuwar fuskantar harin ‘yan ta’adda daga kasar Mali, bayanai ne da aka saba musayarsu yayin tafiyar da aiki a tsakanin hukumomin tsaro, wadanda mutane ba sa bukatar su tayar da hankalinsu akai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.