Isa ga babban shafi
Najeriya - Tsaro

Bakin 'yan ta'adda na shirin kai hare-hare a Abuja - Rahoto

Hukumar kula da shige da fice ta Najeriya ta fitar da wata sanarwa da ke gargadin cewar za a iya kai hare-haren ta'addanci a Abuja babban birnin kasar, a tsakanin ranakun 17 zuwa 31 ga watan Disamban nan.

Wani yanki a Abuja, babban birnin Najeriya.
Wani yanki a Abuja, babban birnin Najeriya. © REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Sanarwa mai dauke da sa hannun kwamandan sintiri a kan iyakokin kasa na hukumar ta shige da fice, Edirin Okoto, ta ce ta samu rahoton barazanar ce daga fadar shugaban kasa dangane da hare-haren da ‘yan ta’adda daga kasashen waje ke shiryawa kan Najeriya.

Kwamanda Okoto ya ce ‘yan ta’addan, sun shirya shiga Najeriya ne daga Mali ta hanyar bi ta cikin Jamhuriyar Nijar.

Wata motar 'yan sandan Najeriya
Wata motar 'yan sandan Najeriya Kola Sulaimon AFP

Wadanda ake zargi da shirya kai hare-haren ta’addancin a Abuja dai sun hada da Drahmane Ould Ali, wanda aka fi sani da Mohammed Ould Sidat dan kasar Aljeriya, tare da wani mai suna Zahid Aminon dan kasar Nijar.

Sanarwar ta kuma ce tuni mutanen biyu da ake zargi suka samu mataimaka akalla 4 ‘yan Najeriya, abinda ya sanya tuni hukumomin tsaro suka kara kintsawa cikin shirin ko ta kwana.

Gargadin hukumar shige da ficen Najeriya ya zo ne makwani kalilan bayan da hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta yi gargadin cewa, ‘yan ta’adda na shirin kai hare-hare kan sansanonin sojin da ke garuruwan kan iyakoki.

Tuni dai hukumomin tsaron Najeriya suka nemi ‘yan kasar da su kwantar da hankulansu, kasancewar a shirye suke wajen dakile duk wata barazana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.