Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan sanda sun ceto mutanen da 'yan bindiga suka sace daga jami'ar Abuja

‘Yan sandan Najeriya sun samu nasarar ceton dukkanin mutanen da ‘yan bindiga suka sace daga rukunin gidajen ma’aikatan Jami’ar birnin Abuja a ranar Talata.

Katangar Jami'ar birnin Abuja dake Najeriya.
Katangar Jami'ar birnin Abuja dake Najeriya. © Daily Trust
Talla

Da safiyar ranar Talatar da ta gabata 2 ga watan Nuwamba gungun ‘yan bindiga suka kutsa kai bangaren gidajen ma’aikatan jami’ar Abuja suka kuma yi awon gaba da mutane shida, ciki har da Farfesa biyu.

Kafin kubutar da su dai sai da ‘yan bindigar suka nemi a biya su kudin fansar da ya kai naira miliyan 300, kafin sakin mutanen da suka yi garkuwa dasu.

Sai dai da safiyar yau Juma’a, wani jami’in jami’ar ta UNIABUJA ya sanar da ceto ma’aikatan nasu ba kuma tare da biyan kudin fansa ba.

Zalika rundunar ‘yan sandan dake kula da shiyyar ta hannun mai Magana da yawunta DSP Josephine Adeh, ta tabbatar da sakin mutanen ba tare da yin karin bayani ba, illa kama wasu dake da hannu a cikin ta’asar da tace an yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.