Isa ga babban shafi
Najeriya

Gwamnatin Buhari ba za ta yi sulhu da 'yan bindiga ba - Monguno

Mai baiwa shugaban Najeriya shawara kan tsaro Manjo Janar Babagana Monguno, ya ce ko kadan gwamnatin Buhari ba ta da sha’awar tattaunawar sulhu da ‘yan bindigar da suka addabi sassan kasar da kisan gilla da kuma satar mutane don kudin fansa.

Mai ba da shawara kan harkokin tsaro Babagana Monguno tare da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a fadar gwamnati da ke birnin Abuja.
Mai ba da shawara kan harkokin tsaro Babagana Monguno tare da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a fadar gwamnati da ke birnin Abuja. © Twitter@NGRPresident / Presidency Nigeria
Talla

Yayin ganawa da manema labarai a garin Abuja ranar Alhamis 11 ga watan Maris, Munguno ya sha alwashin cewar gwamnatin Najeriya za ta yi amfani da cikakken karfi wajen murkushe ta’addancin ‘yan bindiga, tare da gargadin cewa babu wata kungiya da za ta tilastawa gwamnati yin sulhu da dukkanin wasu ‘yan ta’adda.

Mai ba da shawarar kan harkokin tsaro, ya kuma bayyana rashin yawan jami’an tsaro da bukatar karin kayayyaki aikinsu a matsayin wasu daga cikin dalilan da suke haifar da cikas ga kokarin gwamnati na kawo karshen matsalolin tsaron Najeriya. Sai dai ya bayyana kwarin gwiwar cewa sauyin hafsoshin tsaron da aka yi zai taimaka wajen samun nasarar fita daga cikin kangin na rashin tsaro.

Cikin makon nan, shugaban Najeriya Muhammadu ya baiwa ‘yan bindigar dake ta’addanci a Zamfara wa’adin watanni 2 da su gaggauta tuba, ko kuma sun fuskanci fushin gwamnati. Buhari ya bada wa’adin ne bayan umarnin aikewa da Karin sojoji dubu 6 da yayi zuwa jihar ta Zamfara domin murkushe ‘yan bindiga.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.