Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan bindiga sun bukaci biyan kudin fansar marayun da suka sace a Abuja

‘Yan bindigar da suka sace wasu marayu daga gidan da ake kula da su a birnin Abuja dake Najeriya sun bukaci a biyan diyyar naira miliyan 10 akan kowanne maraya guda kafin sakinsa.

Hoto mai wakiltar 'yan bindiga.
Hoto mai wakiltar 'yan bindiga. Jakarta Globe
Talla

‘Yan bindigar sun kuma bukaci biyan naira miliyan goma kan mai gadin gidan da wani magidanci Momoh Jimoh da iyalinsa, da kuma wata mata Rukaiyat Salihu.

Wata majiya a gidan marayun ta shaidawa Jaridar Daily Trust cewar, ‘yan bindigar sun buga waya a ranakun Lahadi da jiya Litinin domin neman diyyar.

Wani dan uwan magidancin da aka sace ya tabbatar da bukatar biyan diyyar, sai dai rundunar ‘yan sandan Abuja bata ce komai ba dangane da bukatar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.