Isa ga babban shafi
Najeriya

Mayakan Boko Haram sun sauya akalarsu zuwa Nasarawa - Gwamna

Gwamnan jihar Nasarawa dake arewacin Najeriya Abudullahi Sule, ya koka kan cewar mayakan Boko Haram na yin tururuwa zuwa jiharsa, abinda ke taka rawa wajen karuwar barazanar rashin tsaron da suke fuskanta.

Gwamnan jihar Nasarawa Abdullahi Sule yayin gaisawa da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Gwamnan jihar Nasarawa Abdullahi Sule yayin gaisawa da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari Twitter@BashirAhmaad
Talla

Gwamna Sule ya bayyana haka ne yayin ziyarar da ya kaiwa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a Abuja, inda yayi masa karin bayani kan sabuwar matsalar tsaron da ta kunno kai.

Yayin ganawa da manema labarai, Gwamnan na Nasarawa ya ce adadin mayakan na Boko Haram da dama ne ke kwarara zuwa jihar tasa, wadanda a baya ‘ya’yan ne ga kungiyar Darussalam da gwamnati ta kora daga jihar Niger da suke makotaka.

Sule ya ce bayan kawar da mayakan daga karamar hukumar Toto, gami da kama 900 daga cikinsu, bayanai sun nuna ‘yan ta’addan sun koma kan iyakar jihar da Benue, inda suka kai hare-hare.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.