Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan bindiga sun sace marayu 8 a gidan da ake kulawa da su a Abuja

A Najeriya Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu satar mutane ne sun mamaye gidan marayu na Rachael da ke Abuja, inda suka sace marayu bakwai, ciki har da mai gadin gidan.

Alamun 'yan bindiga masu garkuwa da mutane a Najeriya
Alamun 'yan bindiga masu garkuwa da mutane a Najeriya Daily Trust
Talla

Rahotanni sun ce, maharan dauke da muggan makamai da sukayi aikinsu cikin sirri, su kuma kutsa wani gida dake makwabtaka da na marayun, kuma sunyi awon gaba da mata uku, amma suka bar maigidan.

Wani mazaunin yankin wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 1 na daren Asabar.

Shugaban karamar hukumar, Alhaji Abdulrahman Ajiya, ya tabbatar wa jaridar Daily Trust aukuwar lamarin, inda ya ce ya sanar da jami’an tsaro.

Itama kakakin rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, ASP Maryam Yusuf, ta tabbatar da faruwar lamarin, duk da cewa ta yi ikirarin cewa mutane shida ne aka sace yayin da mutum daya ya samu kubuta.

Ta ce rundunar ta tura mutanen ta cikin dajin don tabbatar da cewa an ceto sauran wadanda lamarin ya rutsa da su ba tare da ko kwarzane ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.