Isa ga babban shafi
Zamfara

'Yan bindiga sun sace mutane da dama a karamar hukumar Maru

'Yan bindiga sun kai hari  yankin Ruwan Doruwa da ke karamar hukumar Maru a jihar Zamfara, inda suka kashe mutane hudu tare da sace wasu da dama.

Hoton domin misali kan 'yan bindiga.
Hoton domin misali kan 'yan bindiga. © Depositphotos
Talla

Wata majiya a yankin, ta ce ‘yan bindigar sun afkawa garin ne da sanyin safiyar ranar Juma'a, inda suka fara harbi ba kakkautawa, lamarin da ya tilastawa jama’a tserewa, daga bisani kuma bayan kashe mutane 4, maharan suka rika bi gida gida suna zakulo mutane domin yin garkuwa da su.

Ba a dai tantance adadin mutanen da ‘yan bindigar suka sace daga yankin na Ruwan Dorawa ba, sai dai wata majiyar ta bayyana fargabar yawansu ka iya zarta 50.

Jami’an tsaron Najeriya dai sun sha kaddamar da farmaki ta kasa da sama kan sansanonin ‘yan bindigar da suka addabi mazauna sassan yankin arewa maso yammaci da tsakiyar kasar, amma. hakan bai hana ci gaba da fuskantar hare-harensu na kisa da satar mutane ba.

A baya bayan nan, jihohi hudu a yankin arewa maso yammacin Najeriya, ciki har da Zamfara, suka kafa takunkuman da suka hada da takaita zirga-zirgar babura, da sayar da mai da kuma dakatar da cin manyan kasuwanni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.