Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya ta zama kasa ta 5 da ta fi karbar bashi - Bankin Duniya

Bankin Duniya ya bayyana Najeriya a matsayin kasa ta biyar da ta fi karbar bashi daga gare shi, bayan da gwamnatin kasar ta ciwo bashin dala biliyan 11 da miliyan 700, kwatankwacin kimanin naira tiriliyan 4 da biliyan 816.

Wani yanki na garin Onitsha da ke kudancin Najeriya
Wani yanki na garin Onitsha da ke kudancin Najeriya © Pius Utomi Ekpei/AFP/Getty Images
Talla

Bayanin na kunshe ne cikin sabon rahoton da Bankin Duniyar ya fitar kan kasashe 10 da suka fi fuskantar hatsarin bashi a duniya.

Rahoton Bankin Duniyar ya bayyana India a matsayin kasar da ke kan gaba a tsakanin masu karbar bashin, inda a yanzu haka nauyin da ke kanta ya kai dala biliyan 22, sai Bangladesh a matsayi na biyu bayan karbar jumillar bashin dala biliyan 18, yayin da Pakistan ke da nauyin bashin dala biliyan  16 da kusan rabi.

Sauran kasashen dake matakai biyar na farko sun hada da Vietnam mai dauke da nauyin bashin dala biliyan 14, sai kuma Najeriya mai bashin dala biliyan 11 da miliyan 700.

Bankin Duniya.
Bankin Duniya. Daniel SLIM AFP/File

Dalar Amurkan biliyan 11 da miliyan 700 kwatankwacin naira tiriliyan 4 da biliyan 816 da ke Najeriya, kusan kashi daya bisa uku na kasafin kudin kasar ne na shekarar 2021 wanda ya kai Naira tiriliyan 13 da biliyan.

Kasashen Afirka da ke bin bayan Najeriya wajen nauyin bashin Bankin Duniyar da ke kansu sun hada da Habasha mai dala biliyan 11 da miliyan 200, Kenya mai dala biliyan 10 da miliyan 200, sai Tanzania mai dala biliyan 8 da miliyan 300.

Kasa ta 9 wajen nauyin bashin a Afirka ita ce  Ghana mai dala biliyan 5 da miliyan 600, sai Uganda da ke da bashin dala biliyan 4 da miliyan 400.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.