Isa ga babban shafi
Najeriya - Katsina

'Yan bindiga sun yi awon gaba da Alkali daga kotu a Katsina

Rahotanni daga jihar Katsina a Najeriya, sun ce ‘yan bindiga sun kutsa cikin wata kotu a kauyen Bauren Zakat dake karamar hukumar Safana inda suka sace Alkali.

Hoton domin misali kan 'yan bindiga.
Hoton domin misali kan 'yan bindiga. © Depositphotos
Talla

Babu karin bayani kann daililin da ya sanya Alkalin zuwa kotun da aka yi awon gaba shi, la’akari da cewar dukkanin ma’aikatan shari’a a Najeriya na cikin yajin aikin sai baba ta gani domin neman wasu jerin hakkoki daga gwamnati.

Wasu da suka shaida aukuwar lamarin sun shaidawa jaridar Daily Trust da ake wallafa ta a Najeriya cewar, ‘yan bindigar sun kutsa kai cikin kotun ta Bauren Zakat ne da misalin karfe 3 na yammacin ranar Talata inda suka sace Alkalin mai suna Alhaji Hussaini Sama’ila.

Katsina dai na cikin jihohin yankin arewa maso yammacin Najeriya da suka fi fuskantar hare-haren 'yan bindiga dake kashe rayuka tare da satar jama’a domin kudin karbar kudin fansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.