Isa ga babban shafi
Najeriya - Katsina

Katsina: 'Yan bindiga sun kai hari a karamar hukumar Safana

Rahotanni daga jihar Katsina a tarayyar Najeriya sun ce ‘yan bindiga sun kashe mutane fiye da 10, yayin da suka akalla 3 suka jikkata,yayin farmakin da suka kai kan wani yankin karamar hukumar Safana.

Hoton domin misali kan 'yan bindiga.
Hoton domin misali kan 'yan bindiga. © Depositphotos
Talla

Sai dai yayin ganawa da manema labarai a garin Katsina, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar SP Gambo Isah, y ace mutane 3 ‘yan bindigar suka kashe ba fiye da 10 ba, kamar yadda aka rika yada rahotanni.

Ana dai kyautata zaton cewar ‘yan bindigar sun kai harin a daren jiya Asabar ne domin daukar fansar kashe wani mai taimaka musu da bayanai da wasu mazauna garin Tsatskiya dake karamarhukumar ta Safana suka yi.

Jihar Katsina na daga cikin jihohin yankin arewa maso yammacin Najeriya masu fama da matsalar tsaron hare-haren ‘yan bindiga da kuma satar jama’a da dabbobi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.