Isa ga babban shafi
Najeriya-Katsina

'Yan sa kai sun kashe 'yan bindiga 30 a jihar Katsina

Rahotanni daga Jihar Katsina da ke Najeriya sun ce wasu 'yan sa kai a kauyen Majifa da ke karamar hukumar Kankara sun yi nasarar kashe akalla 'yan bindiga 30 da suka addabe su sakamakon kwantar baunar da suka musu a daren litinin din da ta gabata.

Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari
Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari Daily Trust
Talla

Jaridar Daily Trust da ake wallafawa a Najeriya ta ce, 'yan sa kan tare da mazauna kauyen sun samu labarin shirin kai musu hari, abinda ya sa suka yi shiri, kuma sun yi sa’ar kashe wasu daga cikin maharan.

Wani shaidar gani da ido ya ce maharan cikin dare bisa ababan hawa, wasu harda rakuma sun koma inda suka kwashe gawarwakin yan uwan su da aka kashe.

Jaridar ta ce an samu irin wannan artabu a kauyukan 'yan marafa da Mununu da ke karamar hukumar Faskari inda aka kashe mutane da dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.