Isa ga babban shafi
Najeriya - Katsina

Masallata 30 daga cikin 40 sun kubuta daga 'yan bindiga a Katsina

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da sace mutane 40 da ‘yan bindiga suka yi a karamar Hukumar Jibiya dake jihar Katsina, a yayin da suke tsaka da gabatar da Sallar Tahajudd.

Wani ofishin 'ya sanda a Najeriya.
Wani ofishin 'ya sanda a Najeriya. AFP
Talla

Sai dai jim kadan bayan aika aikar hadin gwiwar jami’an tsaro da suka hada da ‘yan sanda,  sojoji da kuma ‘yan sa kai sun samu nasarar kubutar da mutane 30 daga cikin 40 din da aka sace, kamar yadda kakakin rundunar ‘yan sandan na jihar Katsina SP Gambo Isah ya tabbatar.

Kakakin ‘yan sandan ya kara da cewar babu tabbacin cewa ragowar mutane 10 da ba a ceto ba suna hannun ‘yan bindigar, mai yiwuwa sun tsere ne.

‘Yan bindiga sun sace mutanen 40 yayin da suke tsaka da gabatar da Sallar Tahajjud a wani Masallaci dake karamar hukumar Jibia cikin daren ranar Lahadi wayewar garin yau Litinin.

Wani mazaunin yankin da ya ya shaidawa sashin Hausa na RFI cewar lamarin ya auku ne a yankin Abbatuwa dake garin na Jibiya.

Wani da ya tsallake rijiya da baya yace lokacin da ‘yan bindigar suka kai farmakin, sun zagaye Masallacin ne inda wasu suka shiga suka kashe na’urar amsa kuwwar da ake amfani da ita  ana tsaka da gabatar da Sallah, daga nan suka baiwa mutane umarnin fita waje, suka kuma yi awon gaba da adadin akalla 40.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.