Isa ga babban shafi
Najeriya - Kano

Kano: Sojoji sun cafke 'yan ta'adda a unguwar Hotoro

Jami’an sojin Najeriya sun kai samame kan wani gida a unguwar Hotoro dake jihar Kano, inda suka tasa keyar wasu mutane a yankin Filin Lazio bisa zarginsu da kasancewa ‘yan ta’adda ko kuma wadanda suke da kwakkwarar alaka da ta’addancin.

Wasu sojojin Najeriya a yayin aikin sintiri a Najeriya.
Wasu sojojin Najeriya a yayin aikin sintiri a Najeriya. REUTERS/Afolabi Sotunde/File Photo
Talla

Wasu mazauna yankin sun shaidawa majiyarmu cewar mutanen da aka cafke 13 basu dade da tarewa a wani sabon gida da suka saya ba, tun bayan tarewar tasu kuma aka soma shakku akansu la’akari da yanayin rayuwarsu wajen narkar da dukiya.

Bayanai sun ce sojojin Najeriya sun dirarwa wadanda ake zargin ne da misalin karfe 9 na daren jiya Asabar, inda  suka tasa keyar mutanen ba tare da fuskantar wata turjiya ba.

Yayin tabbatar wa da sashin Hausa na RFI aukuwar lamarin a wata zantawa ta wayar tarho mai magana da yawun rundunar sojin Najeriya na kasa Birgediya Janar Muhammad Yarima, ya yabawa al'ummar jihar Kano kan hadin kan da suke baiwa jami'an tsaro, matakin da ya ce shi su ke bukata daga daukacin 'yan Najeriya domin samun nasara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.