Gwamnatin Zamfara ta musanta ceto 'Yan matan sakandaren Jangebe
A Najeriya, Gwamnatin jihar Zamfara ta musanta rahotannin ceto ‘yan matan sakandaren Jangebe, inda tace har yanzu tana kan ƙoƙarin ganin an sako ɗaliban sama da 300 da ‘yan bindiga suka sace.
Wallafawa ranar:
Sanarwar da fadar gwamnatin jihar ta fitar a dazunan ta ƙaryata rahotannin maban-banta da ke cewa an sako ɗaliban.
Tun a tsakiyar daren Juma'a ne ƴan bindigar suka kustsa makarantar sakandaren kwana ta Mata kuma suka yi awon gaba da ɗaliban 317.
Majalisar Dinkin Duniya, da gwamnatocin kasashen Amurka da na Birtaniya duk sun bayyana harin da aka kai a makarantar sakandaren 'yan mata da ke Jangebe a matsayin abin ban tsoro tare da yin kira da a sake su ba tare da bata lokaci ba.
Ana samun ra'ayoyi maban-banta kan biyan kudin fansa domin ceto munaten da 'yan bindiga ke garkuwa da su, inda ake cewa shine ummul aba'isin yawaitan lamarin, yayin da wasu ke ganin babu sauran dabara muddun akayi garkuwa da mutane face biyan kudin da kare lafiya da rayuwar wadanda aka sace.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu