Isa ga babban shafi
Najeriya

Shugaban wani gungun "Yan bindiga a Zamfara ya mika wuya

Shugaban 'yan bindigar da suka sace daruruwan daliban makaranta a arewa maso yammacin jihar Katsina a watan Disambar daya gabata ya Mika wuya ga mahukuntan jihar Zamfara.

Wasu daga cikin makaman da yan bindiga suka mika zuwa hukuma a Zamfara
Wasu daga cikin makaman da yan bindiga suka mika zuwa hukuma a Zamfara REUTERS/Goran Tomasevic/File Photo
Talla

Abokin aikinmu Faruk Mohammad Yabo ya halarci taron mika makamai da ‘yan bindigar suka yi a fadar gwamnati jihar Zamfara.

Shidai Wannan kasurgumin dan bindigar mai suna Auwalun Daudawa ya Mika wuya ne ga mahukuntan jihar Zamfara ranar Litinin inda suka mika bindigogi kirari AK47 akalla 20 da bindigar RPG ko mai jigida a fadar gwamnatin jihar Zamfara

Auwalun Daudawa ya mika makaman ne tare da daukar rantsuwa da alƙur'ani cewar ba za su koma aikata kisan mutane ba.

"Akan zaman lafiya ne kuma ba tsoro ne yasa muka mika makamai ba, Allah dai ya nuna mana hanya ta gaskiya yasa na dauko makamai na mika su ga hukuma, fatan mu shine a yafe mana laifukan da muka yi a baya"

Auwalun Daudawa ya jagorancin wasu mambibinsa guda 6 ne da suka aiwatar da sace dalibai a kankara ta jihar Katsina a wurin mika makaman abinda ya ja hankalin hukumomin kasa da kasa, da kula kara tankiyar rashin tsaro da yankin arewa maso yammacin Najeriya yake fama dashi.

Gwamnan Jihar Zamfara Bello Muhammad Matawalle dai ya kafe akan cewar sulhu shine kawai mafita a wannan. Matsala.

"Saboda haka wannan shine ake kuma don ya nuna ya fita wannan laifin ya ce baya so ya koma cikin Daji ya fi so ya zauna nan cikin gari, kuma ya ce baya son ko kwabo ga kowa"

Masana harkokin tsaro irin su Squadron Leader Aminu Bala Sokoto na ganin bai kamata a bar su haka kawai ba tare da daukar matakin shari'a ba.

"Ahh, to, abin da annan, mika wuya iri biyu ne akwai wanda zaisha wuya wurin fafatawa ya ce ya mika wuya, wannan ya kamata a hukunta shi, akwai kuma wanda zai ce ya mika wuya bisa radin kanshi, wannan bai kamata a hukunta shi ba"

Captain Y J Umar mai ritaya na ganin ya kamata mahukuntan dake sulhu da yan bindigar su sa hikima a ciki.

"Idan ba'a hukunci, to gaskiya fa, kasar nan za mu ci gaba da samun matsala, saboda amfanin hukunci shine zai zama gargadi ga wadanda ma basu shiga ta'addancin ba, dole ne a je Kotu"

Daudawa, dan shekara 43, dan fashi ne da ya rikide ya koma barawon Shanu daga bisani ya koma dan bindiga mai satar mutane don karbar kudin fansa.

Ya kuma shahara wajen safarar makamai daga Kasar Libiya ya kuma samu horo daga masu kirarin jihadi.

Mazauna jihar Zamfara dai na da mabanbantan ra'ayoyin dangane da wannan mataki da yan bindigar suka dauka.

"A'ahh Akwai jin dadi, don za ka yi murna da mutumin da yayi wa kasa tawaye ya zama dan ta'adda ya dawo ya ce ya daina aikata laifin".."In dai har da gaske sukai yana da kyau a duba saboda dai a samu zaman lafiya a cikin kasarmu"

Yankin arewa maso yammacin Najeriya dai ya sha fama da hare haren yan bindiga da masu satar mutane don karbar kudin fansa tare da kai hare hare na kisan mutane da kona gidaje inda ko a karshen makon daya gabata an yi garkuwa da wasu mutane 19 lokacin da yan bindigar suka kai hari a arewa maso yammacin jihar Kaduna.

Kuna iya latsa alamar sauti da kuke gani domin sauraron rahoton Faruk Yabo

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.