Isa ga babban shafi

Najeriya: 'yan sanda sun tabbatar da sace mutane 6 'yan gida daya a Zamfara

‘Yan sanda a jihar Zamfara dake Najeriya sun tabbatar da sace mutane 6, ‘yayan wani mutum mai suna Sani Gyare da ‘yan bindiga suka yi, da wani karin mutum guda a kauyen Kadauri na karamar hukumar Maru ta jihar.

Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle
Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle premiumtimesng
Talla

Kakakin rundunar ‘yan sandan, Shehu Mohammed ya tabbatar da aukuwar lamarin ga kamfanin dillancin labaran Najeriya ranar Juma’a a Gusau, in da ya sha alwashin ceto mutanen.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ya ruwaito cewa dimbim ‘yan bindiga ne suka afka wa kauyen da sanyin safiyar Juma’a, inda suka ci Karensu ba babbaka.

Satar mutane don karbar kudin fansa, tare da afka wa kauyuka da makamai ya zama ruwan dare a arewa maso yammacin Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.