Isa ga babban shafi
Najeriya-Zamfara

Mutanen Zamfara na cikin mawuyacin hali - MSF

Kungiyar Agaji ta Medicins Sans Frontier, MSF, ta bayyana matukar damuwa kan halin da mutanen Jihar Zamfara dake Najeriya ke ciki, sakamakon tashin hankalin da ya mamaye sassan Jihar ya kuma yadu zuwa wasu yankunan dake yankin arewa maso yammacin Najeriya.

Wasu 'yan gudun hijira da hare-haren 'yan bindiga ya raba da muhallansu a jihar Zamfara
Wasu 'yan gudun hijira da hare-haren 'yan bindiga ya raba da muhallansu a jihar Zamfara MSF/Abayomi Akande
Talla

Kungiyar wadda ke da asibitin kula da marasa lafiya a Anka da Zurmi da Shinkafi dake Jihar Zamfara tace mutane da dama sun tsere daga gidajen su sakamakon tashin hankalin wanda ke kai ga kisa da kuma sace mutane domin karbar diyya.

MSF tace yanzu haka da dama daga cikin irin wadannan mutane da suka zama Yan gudun hijira, basa samun wani taimako daga hukumomin kasa ko na Jiha, a daidai lokacin da suke bukatar muhimman kayayyakin rayuwa irin su matsugunai da ruwan sha da kuma abinci.

Kungiyar tace matsalar yadda wadannan Yan gudun hijira zasu ciyar da ‘yayan su ya zama abu mai matukar wahala, ganin yadda Yan bindigar suka hana su noma gonakin su saboda barazanar Yan bindigar.

Yanzu haka kungiyar MSF na da asibitin yara mai gado 135 a garin Anka kuma tun daga shekarar 2010 take aiki, abinda ke baiwa mutane daga garuruwan dake kusa da Yankin damar kai yaran su ana duba lafiyar su.

Har ila yau kungiyar tana kula da marasa lafiya a babban asibitin Shinkafi, ciki harda wani sashe mai dauke da gadaje 33 da ake ciyar da marasa lafiya da kuma kula da su, yayin da tace da cibiyar lafiya mai dauke da gadaje 30 a Zurmi.

Kungiyar tace tsakanin watan Janairu zuwa Oktobar tana ta kula da marasa lafiya 20,260 a garuruwan Anka da Shinkafi da Zurmi da kuma Gusau, kuma wasu daga cikin su na dauke da tamowa da cututtuka masu wahalar kula.

Dr Salih Muhammad Auwal na asibitin Shinkafi yace suna karbar akalla yara tsakanin 25 zuwa 30 kowacce rana masu fama da cutar zazzabi mai zafi, abinda ya sa kungiyar ta kara gadajen dake asibitin daga 19 zuwa 54 da kara dakunan aje marasa lafiyar.

Kungiyar ta bukaci kungiyoyin agaji na duniya da gwamnatoci da su kaiwa jama’ar Jihar Zamfara dauki dangane da wannan mawuyacin halin da suka samu kan su domin ceto rayuwar su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.