Isa ga babban shafi

Najeriya: 'Yan bindiga sun kawo tsaiko a zaben cike gurbi a Zamfara

Rahotanni daga jihar Zamfara da ke Najeriya sun ce 'yan bindiga sun kai hari wata tashar zabe dake Oroji a karamar hukumar Bakura inda suka tarwatsa shirin zaben Dan Majalisar Jihar da ake gudanarwa yau Asabar.

Misali na 'yan bindiga.
Misali na 'yan bindiga. Jakarta Globe
Talla

Jaridar Daily Trust ta ruwaito wani mazaunin kauyen, Suleiman Muhammed Rini na cewar lamarin ya auku ne da misalin karfe 8.30 na safe bayan bude tashar zaben domin fara kada kuri’a.

Rini ya ce shi da sauran masu kada kuri’a da kuma baturen zaben sun ranta a na kare domin tsira da rayukansu a lokacin da 'yan bindigar suka fito daga daji.

Bayan shaidawa 'yan sanda da sojoji, jami’an tsaron sun yi nasarar murkushe harin, kafin cigaba da gudanar da zabe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.