Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan bindiga sun halaka mutane 35 a masarauta ta - Sarkin Maru

Akalla mutane 35 ‘yan bindiga suka halaka yayin farmakin da suka kaiwa wasu kauyuka 5 a karamar hukumar Maru dake jihar Zamfara a Najeriya.

Misalin hoton 'yan bindiga da ke addabar al'umma a sassan Najeriya.
Misalin hoton 'yan bindiga da ke addabar al'umma a sassan Najeriya. Information Nigeria
Talla

Yayin karin bayani ga gwamnan jihar Bello Matawalle da ya kai ziyarar jaje, Sarkin Maru Alhaji Abubakar Gado Maigari, ya ce kauyukan da ‘yan bindigar suka kaiwa hari sun hada da Asha-Lafiya, Munkuru, Mahuta, Rayau da kuma Dutsin Gari.

Sarkin ya shaidawa gwamnan na Zamfara cewar yanzu haka al’ummar dake zaune a kauyukan na bukatar agajin gaggawa, saboda mawuyacin halin da suke ciki, a dalilin rashin tsaro.

Zamfara na daga cikin jihohin arewa maso yammacin Najeriya masu fama da hare-haren ‘yan bindiga da satar jama’a don kudin fansa, matsalolin da suka zama ruwan dare a sassan jihohin Katsina, Kaduna da kuma Sokoto.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.