Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan bindiga sun kaiwa tawagar Sarkin Kauran Namoda farmaki

‘Yan bindiga sun kaiwa tawagar motocin Sarkin Kaura Namoda Alhaji Sunusi Muhammad dake jihar Zamfara farmaki, inda suka halaka akalla mutane 8, tare da jikkata wasu da dama.

'Yan bindiga sun yiwa tawagar daya daga cikin sarakunan Zamfara kwanton Bauna
'Yan bindiga sun yiwa tawagar daya daga cikin sarakunan Zamfara kwanton Bauna Jakarta Globe
Talla

Wani da ya tsira daga farmakin ya ce ‘yan bindigar sun yiwa tawagar Sarkin kwanton Bauna ne akan hanyar Zaria zuwa Funtua, lokacin da suke kokarin komawa garin Gusau daga Abuja.

Bayanai sun ce cikin wadanda suka rasa rayukansu a farmakin akwai direba guda da kuma ‘yan sanda uku, sai dai Sarkin na Kaura Namoda ya tsira ba tare da samun rauni ba.

Rundunar ‘yan sandan Najeriya dake Katsina ta tabbatar da aukuwar lamarin sai dai ba ta yi karin bayani akai ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.